NOORIL MUSTAPHA (1)

 NOORewardsRIL MUSTAPHA

Contents

ABUBUWANDA YA KUNSA


GABATARWA

JAWABIN MAWALAFI 

SADAUKARWA

SUNAYENSA

INKIYA DA AKEYIMAI

NASABARSA

NOOR-E-MUSTAPHA

MU’UJIZAR HAIHUWARSA

HAIHUWA MAI ALBARKA

YARINTARSA

TSAGEWAN KIRJINSA

SAU NAWA TSAGEWAN KIRJINSA

WAFATIN NANA AMINA

ZAMANSA AGUN ABU DALIB

TAFIYARSU ZUWA SHAM NA FARKO    

YAKIN FUJAR

HALTIL FUDHUR

TAFIYARSU ZUWA SHAM NA BIYU

AURENSA DA NANA KHADIJA

KASUWANCINSA

WAHAYI NA FARKO

DA’AWA 1-2-3

DAN SAKO GA ABU DALIB

HIJRA ZUWA GA HABASHA

YANKEWAR ZUMUNTA

SHEKARAN BAKIN CIKI

AQABA TA FARKO

AQABA TA BIYU

HIJRA ZUWA MADINA

TARUWAN KAFIRAI

HIJRA

KYAUTAR RAKUMA DARI

DOKIN SURAQATA

ANNABI SALLALAHU ALAIHI WASSALLAM A MADINATU MUNAWWARA.

 GABATARWA

Da sunan ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI.

TSira da aminci sukara tabata bisa masoyinmu annabi Muhammad [sallallahu alaihi wassallam] da alayensa da sahabansa da tabi’ai da tabi,e tabi’inda masu bin tafarkinsa izuwa ranar tashin alqiyama.

Wanan litafi ne da ya tatara bayani na rayuwar fiyayen haliita ANNABI MUHAMMADU [SALLALLAHU ALAIHI WASSALLAM] Tin daga haihuwarsa izuwa hijrarsa zuwa madina.

JAWABIN MAWALLAFI

Wanan litafin asalinsa an wallafashi da yaren English language sai naga ya cancanta da in fasarashi da hausa domin en uwa musulmi masoya fiyayen halite [sallallahu alaihi wassallam] domin mu amfana mu samu albarka dake cikin wanan karatun, sananan abinda ya karfafani da wananan litafin shine da yawan tarihin daga sahihan hadisa aka cirosu daga jiga jigan sahabai da manyan malluma. Ina mana fatan ALLAH ya amfanar damu da duk abinda zamu karanta daga wananan tarihi mai suna [HASKEN ZABBABE] UBANGIJI yakara mana soyaya da qaunarsa fiyayen halite [sallallahu alaihi wassallam.

SADAUKARWA   

Na sadaukar da wanan litafi hadiya ga SAYYIDINA RASULLULLAH [SALLALLAHU ALAIHI WASSALLAM].


FARAWA


YAWAN SUNAYENSA


Masoyinmu RASULULLAHI [sallallahu alaihi wassallam] yana da sunaye dayawa wanda ake kiransa dashi. A sama an sanshi da [AHMAD DA MAHMUD] sanan a duniya an sanshi da [MUHAMMADU,sallallahu alaihi wassallam],a cikin ataurah Annabi[sallallahu alaihi wassallam] ana kiransa da AHMADU, SAHOOK,DA QATAAL. Acikin injila ana kiransa da HAMID. Wadansu sufaye sunce akwai sunayen Allah guda dubu daya[1000] da sunayen Annabi guda dubu daya [1000] .[zirkani kasha na uku babi na 113].


 INKIYA DA AKE YIMAI

 

Masoyinmu [sallallahu alaihi wassallam]yana da wasu inkiya da akeyimai kamar,Abu Qasim da Abu Ibrahim. Mala’ika jibrilu [alaihi ma’a nabiyina sallam] idan yazo wajansa yana ce masa Assalamu allaika ya Abal Ibrahim. [ZIRKANI BUGU NA 3 BABI NA 150].

 NASABARSA


NASABARSA TA WAJAN MAHAIFINSA


Nasabarsa ta wajan mahaifiyarsa shine kamar haka ; MUHAMMADU[SALLALLAHU ALAIHI WASSALLAM] dan Abdullahi [R TA] dan Abdul mudalab , dan hashim ,dan Abdul munafi, dan qusayyyu,dan kilabi ,dan murrata,dan luwa’I, dang alibi, dan fihiri,dan malik,dan mudrikita,dan kinanata, dan khuzaimata,dan mudrikita, dan iliyas,,dan muzari,dan nazari, dan ma’adi,dan adnan. [BUKHARI SHAREEF]


 NASABARSA TA WAJAN MAHAIFIYARSA

Nasabarsa ta wajan mahaifiyarsa AMINATA [R T A] shine Annabi MUHAMMADU [SALLALAHU ALAIHI WASSALLAM] dan Aminatu [R T A] yar wahab, dan Abdul munafi ,dan zahrata,dan kilabi, dan murata. Dukansu wadanan gidaje ko zuri’ar sun fito ne daga kilabi dan murata.sanan dukansu sun zama adnan, an karbo adnan yana daga zuri’ar ANNABI Isma’ila , shi Annabi isma’ila dan Annabi Ibrahim ne.[MADARIJUN NUBUWAT KASHI NA 2 BABI NA 14].

Wannan yana nuna manzan ALLAH [SALLALLAHU ALAIHI WASSALLAM] yana daga dangi Annabi Ibrahim, daga kowani bangaren iyaye, masu tarihi sun nuna ceiwa duka kakanin manzon Allah [sallallahu alaihi wassallam,]tsarkakaka ne. [ibn sa’ad].A


NOOR-E-MUSTAPHA [HASKEN ANNABI]

Kafin halitan hasken ANNABI [SALLALLAHU ALAIHI WASSALLAM] ubangiji wani taska ne boyaye, da ALLAH yaso a sanshi sai ya halici hasken ANNABI MUHAMMADU [SALLALLAHU ALAIHI WASSALLAM], daga hasken Annabi Muhammad [sallallahu alaihi wassallam] ALLAH ya halice lauhul mahfuz ,alqalamin qudura,al arshi ,kursiyu, da wuta, da aljahna. Yazo acikn hadisul qudsi Allah [subhanahu wata’ala]yace , inbadan na halice muhammadu [sallalahu alaihi wassallam] ba da ban halici Annabi Adam ba, da ban halice al-jahna da wuta ba, in badan na halice shi ba da ban halice halita ba da ban halice duniya ba. Annabi [sallallahu alaihi wassallam] yace A llah mai girma yafara halice [haskena],sanan ya halice dukan halta daga haskena , ni kuma daga hasken ALLAH.  

Daga hadisai masu girma wanda aka ambata yazamu fahimci ceiwa Allah mai girma ya fara halice hasken Annabi [sallallahu alaihi wassallam]sanan daga haskensa yahalice duk halita.[raudatun na’im fi zikiril nabiyil karim].

Hasken Annabi [sallalalahu alaihi wassallam] an saka a goshin annabi adam [a s] sanan hasken ye tafiya har izuwa mahaifin Annabi abdullahi [a s] sanan yashiga cikin mahaifiyar Annabi Aminatu [a s],

MU’UJIZA ACIKI NA HAIHUWA

NANA Amina [R A] tace bata ji damuwa ko ciwo ba sanda ta dau cikin ba, a farkon wata na shida ta sake ceiwa bayan wata shida tana jin wani haske na musaman a cikinta, sanan tai mafarki da mala’ika ya sanar da ita ceiwa, tana dauke da Annabin karrshe a cikinta, mala ikan ya sake sanar da ita , in Annbi [sallallahu alaihi wwassallam] in an haifeshi wani haske zai baiyana zai haskaka ginin sham da basra, nana amina [R A] tace lokacin da Annabi [salallahu alaihi wassallam] yazo cikina , wata na farko shine rajab, a wannan wata naga babban mutum mai haske da kamshi a cikin mafarkina , sai na tambayeshi wanene, sai yace shine Annabi adamu, sai tambayeshi dalilin zuwansa, sai yace na zo in miki bishara mai kyau kina dauke da cikin shugaban duniya, a wata na biyu naga Annabi sheesu , a wata na uku naga Annabi idrisu, a wata na hudu naga Annabi nuhu, a wata nan a biyar Annabi huddu, a wata na shida naga Annabi ibrahimu , a wata na bakwai Annabi isma’ila , a wats na takwas Annabi musa , a wata na tara Annabi isa , sannan kowane su da bishara mai kyau. [raudatun na emm]


MAFI ALBARKAN HAIHUWA A CIKIN HALITA

Masoyin mu Rasulullahi [sallallahu alaihi wassallam] shugaban halite an haifeshi ranar litini sha biyu [12] ga watan rabi’il auwal ,shekara hamsin da uku[53] kafin hijra, wanda ye deide da ishirin ga wata aprilu shekara dari biyar da saba’in da biyar [571 AD] lokacin a subahi . yazam al’ada Na mutanin Makkah zuwa ziyara gidan haihuw

Comments