NOORIL MUSTAPHA 2
Rewards YARINTARSA
A karamin sa , Annabi [sallallahu alaihi wassallam] an ba da shi raino a wajan halimatu sa’adiya [R A] wanan al’ada ce ta larabawa, kafin a bata raino , Annabi [sallallahu alaihi wassallam] nana Amina ta shayar dashi, da suwaiba, da Ummu aimana, [R A].
Halimatu sa’adiya [R A] TACE data dauko Annabi [sallallahu alaihi wassallam] zuwa gidanta ba ta taba kuna fitila da dare ba, tin da hasken Annabi [sallalahu alaihi wassallam]ya haskaka yashiga gidanta. Ta kara da ceiwa in tana shayar da Rasulullahi [sallallahu alaihi wassallam] na gefen dama yake kawai yake karba bai ta ba shan na hagu ba, sai yabarwa yaron halimatu sa’adiya na hagun. Ta kara da ceiwa tun yana karami zaka ganshi tsaptatace,tsarkakake,bai ta ba bawali akan gado ba, bai ta ba bukaci ta kurkura masa baki ba,in tayi niyar yima sa sai ta ga anriga an ayi. Nana Halima [R A] tace Annabi [sallalahu alaihi wassallam] ye girma da sauri sannan girmansa yabanbanta da irrin na yara. Ye girma a rana daya,ama sauran yara na girma a wata da wata, wasu na girma a shekara, tace lokacin da yana wata biyu yana iya zama mai kyau, a wata uku yafara tsayawa yana tafiya, a wata na biyar yana tafiya da Magana sarai, farkon Magana da ya fara fada shine; ALLAHU AKBAR ,ALLAHU AKBAR ,ALHAMDULILLAHI RABIL ALAMEEN ‘ NANA [R A] tace , da dare inajinsa yana karanta ‘LAILAHA ILALAHU QUDUSUN NAMATUL UYUN WA RAHMAN , LA TAKHUZHU SINATUN WALA NAUM , tace a wata na shida yafara gudu sanan a watan san a bakwai yana gudu da sauri,a wata na takwas yafara Magana dadada ,a wata na tara yana magana na basira da hikima . nana Halima [R A] tace lokacin da Rasulullahi[sallallahu alaihi wassallam] yana da wata goma yakan iya jifa da kwari da baka,duk lokacin da yara sun kirashi wasa , sai yace dasu Allah bai haliceni inyi was aba.Annabi[ sallallahu alaihi wassallam] yana daukan komai da hanunsa na dama ne, da fadin BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM[RAUDAUTUN NAEMM].
NANA HALIMA [R A]tace akwai wani lokacin fari, sai muka dauki Annabi [sallallahu alaihi wasallam] tare da ni munje wani wuri muni Addu’a da fadin; Ya Allah ka saukar mana da ruwa dan Albarkan wanan yaron. A take sai hadari yafara haduwa sanan an fara ruwa sosai. Nana Halima [R A] ta albarkatu da manzan Allah [sallallahu alaihi wassaallam]sanda yake wajanta. Haka wanan yachi gaba har lokacin shakus sadr[TSAGEWAR KIRJI TSARKAKAKE YAFARU].
TSAGEWAN KIRJINSA
WANI LOKACI NANA Halima [R A] yaron ta yazo da gudu izuwa gida, dan ya fadawa mahaifiyarsa ceiwa, yaga mutani uju masu haske sun saka kaya farare ,suka kwantar da MUHAMMAD[SALLALAHU ALAIHI WASSALLAM] a kasa sun bude masa kirji ‘ sai ya barsu a wanan yanayi ,nazo na kiraku ku temaka ; nana Halima [R A] Ita da mijinta sun ruga da gudu zuwa yadda dabobinsu ke kiwo, suna iso wajan sun sami Rasulullahi[sallalahu alaihi wassallam] yanayinsa ya canza . nana Halima[R A] sai tai mishi Magana cikin nitsuwa ta tambayeshi abinda yafaru, Annabi [sallALAHU ALAIHI WASSALLAM] YACE ‘mutani uku masu haske da kaya farare sun kwantar dani kasa sanan sun sun cire wani abu sai suka sa acikin wani tasa, sais sun mishi stamp ko tambari , duka a wanan lokacin banji wani ciwo ba , nana halimatu [R A] tai kalon Annabi [sallalahu alaihi wassallam] sosai. Lokacin Annabi [sallallalahu alaihi wassallam] yana da shekara biyu, yana da cikaken lafiya sana an daina shayar dashi , nana halima [R A] faruwaan wanan lamarin sai yasa ta dawo dashi gun nana Amina[ R A] ta bata kyautuka[ madarijun nubuwat kasha na biyu babi na goma shabiyu]
SAU NAWA AKA TSAGA KIRJIN SA
Mallam shah abdul aziz muhadith dehlwI [R A] ya rubuta acikin tafseer na alam nashra ,kirjin Annabi [sallalahu alaihi wassallam] an bude kirjinsa har sau hudu. Na farko an bude kirjinsa lokacin da yake ggidan nana Halima[ R A] hikimar bude kirjin shine dan a tsarkake shi daga dabi’a na wassanni irin na yara ,na biyu shine lokacin da Rasullullahi [sallallahu alaihi wassallam] yana shekara goma wananan an bude kirjin saboda a cire masa tsoro a lokacin samartakan sa, na uku yafaru lokacin da yake kogon hira an sa a zuciyar sa saboda saukar da wahayi dagav Allah subhanahu wata’ala , na hudu shine lokacin isra I da mi’eraji , a wananan tafiyar zuciyar Ankara wa kyau haske da basira. Anyi wananan saboda ya kusance ALLAH [SUBHANAHU WATA’ALAH] da sake yin Magana da mahalicinsa [JALA WA’AZA] [MADARIJUN NUBUWAT SEERATUL MUSTAPH].
WAFATIN NANA AMINA [RAHMATULLAHI ALAIHIA]
Lokacin da Annabi [sallallahu alaihi wassallam] yana da shekara shida , mahaifiyarsa ta dauke shi tare da ita zuwa tafiya madina dan su ziyarci en uwansu, su sake je makwancin mahaifinsa, a wana tafiya suna tare da ummu aimana [rahmatullahi alaiha] yayin dawowa ,sun wuce wani wuri da ake kira abwaya, a wajan nana Amina [rahmatullahi alaiha] tayi wafati. Sai ummu aimana ta dawo da manzon Allah [salllallahu alaihi wassallam] a makka, sannan yana hanun kakan sa abdul mudalib [R A] Annabi [sallalahu alaihi wassallam] yana da shekara takwas kakan sa abdul mudalib ye wafati.
ZAMANSA DA ABU DALIB
Bayan wafatin abdul mudalib , Annabi [sallallahu alaihi wassallam] ya dawo karkashin kulawar baffan sa abu dalib. Baffan sa yadauko kyaykyaywan rainon mazon Allah [sallallahu alaihi wassallam] yakarar da duk lokacin sa tare dashi, yana bacci kusa da manzon Allah [sallallahu alaihi wassallam] ,abu yana ceiwa ; ban ta ba ganin Annabi [sallallahu alaihi wassallam] ye karya ba, ko rashin gaskiya da wani ba, ban ta ba ganinsa ye fishi da wani ba, ko zama tsakanin yaran banza ba, bai ta ba yin abin rikici ba, kullum yana cikin girmamawa cikin kamala[seeratul Mustapha babi tamanin da shida /tamanin da
TAFIYAR SU ZUWA SHAM
Annabi[ sallalahu alaihi wassallam] yana da shekara goma shabiyu. Tafiyar abu dalib zuwa sham ya dauki masoyinmu Rasulullah[sallallahu alaihi wassallam] tare dashi. A yayin tafiyar su sun hadu da wani mallami bahira, mallamin ya haddace injila da a taura sanan yasan sufofin annabin karshe . wananan mallamin da ganin abu da dalib da Annabi[sallallahu alaihi wassallam] sai ya nuna yasan Rasulullahi[sallalahu alaihi wassallam] sai ya sanar da abu dalib dalib yana ceiwa; ANNABI [SALLALLAHU ALAIHI WASSALLAM] shine shugaban Annabawa [ alaihimu sallam] sanan Annabi [sallallahu alaihi wassallam] shi rahmatul lil alamin ne,[ma’ana ,rahma ga dukan halite] yakara da ceiwa , ina ganin duwatsu bishiyoyi suna duka mai,sanan girgije yana binsa yana masa inuwa, sanan naga tambarin Annabta asakanin kafadunsa . sai wanan mallamin ya ce da abu dalib da ya koma da Annabi[sallalahu alaihi wassallam] ka koma dashi a Makkah kabar tafiya izuwa sham, ka sayar da kayan kasuwanka anan ana sanan ka tafi .a sham akwai kafirai makiyansa. A lokacin da sun ganshi a sham zasu yin kokarin kasheshi. Sai abu dalib ya dauki Magana bahira , sanan ya koma Makkah da Annabi [sallallahu alaihi wassallam]. [tirmizi shareef kasha na biyu]
Comments
Post a Comment