Posts

NOORIL MUSTAPHA 3

Dayawa fada a tsakaninsu.yin fada da junnansu da kowannensu ,yahada da kashe kashe da rauni cikinsu. Daga tsakakanin yakokin babban cikin su shine; YAKIN FUJJAR ; mutanin larabawa suna ,girmama  watan zil qiddar zil hajj,muharram da rajab,suna jin wani nauyi nayin yaki a cikin wadannan watanni. Suna aje makaman yakin su a wananan wattanni. Sai dai akwai wasu dalilai da bukukuwa da zai zama masu dole suyi yaki a wa enan wattani; larabawa suna kiran wannan HUROOB-E-FUJJAR [YAKIN LEIFUKA], karshen fujjar da akayi shine tsakanin quraishawa da kbilan qais, a wannan lokacin Annabi [sallallahu alaihi wassallam] yana da shekara ishirin [20] ,saboda quraishawa na kan gaskiya akan wannan yakin, Annabi [sallallahu alaihi wassallam] yayi wanan yakin a gefen baffansa abu dalib ,bayan haka Annabi [sallallalhu alaihi wassallam] baiyi fada ba a wanan yakin ba,ya baiwa baffansa takobi .quraishawa sunyi nasara a wanan yakin [seeratul ibn hisham kashi na 2 babbi na dari da tamanin da shida] HALFIL FU...

NOORIL MUSTAPHA 2

Rewards  YARINTARSA A karamin sa , Annabi [sallallahu alaihi wassallam] an ba da shi raino a wajan halimatu sa’adiya [R A] wanan al’ada ce ta larabawa, kafin a bata raino , Annabi [sallallahu alaihi wassallam] nana Amina ta shayar dashi, da suwaiba, da Ummu aimana, [R A]. Halimatu sa’adiya [R A] TACE data dauko Annabi [sallallahu alaihi wassallam] zuwa gidanta ba ta taba kuna fitila da dare ba, tin da hasken Annabi [sallalahu alaihi wassallam]ya haskaka yashiga gidanta.  Ta kara da ceiwa in tana shayar da Rasulullahi [sallallahu alaihi wassallam] na gefen dama yake kawai yake karba bai ta ba shan na hagu ba, sai yabarwa yaron halimatu sa’adiya na hagun. Ta kara da ceiwa tun yana karami zaka ganshi tsaptatace,tsarkakake,bai ta ba bawali akan gado ba, bai ta ba bukaci ta kurkura masa baki ba,in tayi niyar yima sa sai ta ga anriga an ayi. Nana Halima [R  A] tace Annabi [sallalahu alaihi wassallam] ye girma da sauri sannan girmansa yabanbanta da irrin na yara. Ye girma a rana...

NOORIL MUSTAPHA (1)

 NOO Rewards RIL MUSTAPHA Contents ABUBUWANDA YA KUNSA GABATARWA JAWABIN MAWALAFI  SADAUKARWA SUNAYENSA INKIYA DA AKEYIMAI NASABARSA NOOR-E-MUSTAPHA MU’UJIZAR HAIHUWARSA HAIHUWA MAI ALBARKA YARINTARSA TSAGEWAN KIRJINSA SAU NAWA TSAGEWAN KIRJINSA WAFATIN NANA AMINA ZAMANSA AGUN ABU DALIB TAFIYARSU ZUWA SHAM NA FARKO     YAKIN FUJAR HALTIL FUDHUR TAFIYARSU ZUWA SHAM NA BIYU AURENSA DA NANA KHADIJA KASUWANCINSA WAHAYI NA FARKO DA’AWA 1-2-3 DAN SAKO GA ABU DALIB HIJRA ZUWA GA HABASHA YANKEWAR ZUMUNTA SHEKARAN BAKIN CIKI AQABA TA FARKO AQABA TA BIYU HIJRA ZUWA MADINA TARUWAN KAFIRAI HIJRA KYAUTAR RAKUMA DARI DOKIN SURAQATA ANNABI SALLALAHU ALAIHI WASSALLAM A MADINATU MUNAWWARA.  GABATARWA Da sunan ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI. TSira da aminci sukara tabata bisa masoyinmu annabi Muhammad [sallallahu alaihi wassallam] da alayensa da sahabansa da tabi’ai da tabi,e tabi’inda masu bin tafarkinsa izuwa ranar tashin alqiyama. Wanan litafi ne da ya tatara bayani na rayuwa...